3 Disamba 2015 - 09:01
Shugaban kungiyar Taliban ya samu raunana

Hukumomin kasar Afghanistan sun ce an raunana shugaban kungiyar Taliban Mullah Akhtar Mansour a wani rikicin cikin gida tsakanin su lokacin da suke gudanar da taron kwamnadodjin kungiyar.

Sultan Faizi, mai magana yawun mataimakin shugaban kungiyar, yace wasu ya ‘an kungiyar biyar suka mutu a rikicin. Watanni hudu kenan da nada Mansour a matsayin shugaban kungiyar.  

A yan watani da suka gabata an samu barkewar rikici tsakanin bangarorin kungiyar mayakan Taliban da ke gaba da juna a kudancin lardin Zabul a kasar Afghanistan. Mayakan da dama ne aka ruwaito sun mutu a rikicin da ya barke tsakanin masu biyayya ga Mullah Akhtar Mansour da kuma mabiyan Mansoor Dadullah.

Jami’an tsaron Afghanistan sun ce tun a ranar Assabar ne rikicin ya barke, kuma rikicin ya sa an tsinci gawarwakin mutanen kabilar Hazaras da mayakan suka sace a watan Oktoba.288